Home Coronavirus Babu Wanda Ya Sauya Sheka Zuwa PDP – APC

Babu Wanda Ya Sauya Sheka Zuwa PDP – APC

439
0
Babu Wanda Ya Sauya Sheka Zuwa PDP - APC
Babu Wanda Ya Sauya Sheka Zuwa PDP - APC

Jam‘iyyar APC reshen jihar Kwara ta karyata rahotannin da ke cewa, ‘ya’yan jamiyyar dubu 10 sun sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP.

Mai Magana da yawun jam’iyyar na jihar Alhaji Tajudeen Aro ya bayyana haka a cikin wata sanarwar da ya fitar a garin Ilori, inda ya ce labarun da a ke yadawa cewa mutane dubu 10 sun sauya sheka daga APC zuwa PDP karya ce tsagoran ta.

Ya ce, Wannan ikirarin na PDP abin dariya ne, yana mai cewa ta yaya mutane 10,000 za su sauya sheka cikin wannan hali da ake ciki na annobar Korona ba tare da sanin al’umma ba.

Tajudeen Aro ya kuma yi kira ga al’umma su yi watsi da rahotannin karya da jamiyyar adawa ke kokarin amfani da rashin jituwan da ke faruwa a cikin APC wajen bata mata suna.