Home Labaru Wutar Lantarki: Sarkin Zazzau Ya Ce Akwai Bukatar Gwamnati Ta Kara Zage...

Wutar Lantarki: Sarkin Zazzau Ya Ce Akwai Bukatar Gwamnati Ta Kara Zage Damtse

726
0
Alhaji Dakta Shehu Idris, Martaba Sarkin Zazzau
Alhaji Dakta Shehu Idris, Martaba Sarkin Zazzau

Mai martaba Sarkin Zazzau Alhaji Dakta Shehu Idris, ya bukaci gwamnatin tarayya ta yi da gaske game da batun samar da dawwamammiyar wutar lantarki a fadin Nijeriya.

Sarkin ya bayyana haka ne, yayin da ya karbi bakuncin ministan wutar lantarki Injiniya Mamman Saleh da karamin ministan wuta Goody Jedi-Agba a fadar sa dake birnin Zazzau.

Ministocin biyu dai sun isa Zaria ne domin kaddamar da wata tashar wutar lantarki da aka yi wa gyara a cikin jami’ar Ahmadu Bello.

Sarkin ya cigaba da cewa, akwai bukatar gwamnati ta zage damtse wajen samar da ingantacciyar wutar lantarki a Nijeriya, lamarin da ya ce zai kara karfin tattalin arziki tare da kara martabar kasar nan.Da ya ke jawabi yayin kaddamar da tashar wutar, Ministan ya ce yana fatan gyaran da aka yi wa tashar wutar lantarkin zai inganta wutar da ake samu a jami’ar Ahmad Bello.

Leave a Reply