Home Labaru Kin Jinin Baki: Afrika Ta Kudu Ta Turo Jakadu Su Ba Nijeriya...

Kin Jinin Baki: Afrika Ta Kudu Ta Turo Jakadu Su Ba Nijeriya Hakuri

251
0

Shugaban kasar Afrika Ta Kudu Cyril Ramaphosa, ya aiko tawagar jakadu uku zuwa Nijeriya, domin neman sasanci tare da bada hakuri a kan hare-haren da ‘yan kasar su ka rika kai wa ‘yan Nijeriya su na kashe su.

Jakadan dai, zai kara jaddada wa Nijeriya bukatar kara dankon zumunci tsakanin kasashen Afrika, tare da tattauna hanyoyin da za a sake tabbatar da zaman lumana a tsakanin kasashen biyu.

Rahotanni sun Ambato Kakakin Shugaba Ramaphosa Khusela Diko ya na cewa, jakadun uku za su fara kai ziyara Nijeriya sannan su karasa wasu kasashen Afrika shida.

Ya ce za su isar da sakon Shugaba Ramaphosa dangane hare-haren da aka kai wa ‘yan kasashe da ke zaune a Afrika ta Kudu tare da lalata masu dukiyoyi da aka yi. Dangantaka a tsakanin Afrika Ta Kudu da Nijeriya dai ta yi tsami, biyo bayan hare-hare da kisan da aka rika yi wa ‘yan Nijeriya a can.