Home Labaru Ilimi Gudunmuwar Ilimi: Gbajabiamila Ya Isa Katsina Domin Koyar Da Daliban Sakandare

Gudunmuwar Ilimi: Gbajabiamila Ya Isa Katsina Domin Koyar Da Daliban Sakandare

454
0

Shugaban majalisar wakilai Femi Gbajabiamila, zai koyar a babbar makarantar sakandare ta ‘Pilot’ da ke kofar Sauri a cikin birnin Katsina.

Gbajabiamila dai ya fara aikin koyarwa ta sa-kai a mazabar sa ta Surelere da ke Legas a shekara ta 2017, lokacin ya na rike da mukamin shugaban masu rinjaye a zauren majalisa.

Mai taimaka wa Gbajabiamila ta fuskar yada labarai Lanre Lasisi,, ya ce shugaban majalisar zai koyar a makarantun sakandare na dukkan sassan Nijeriya.

Lasisi, ya ce Gbajabiala zai koyar da daliban makarantar sakandare ta unguwar Kofar Sauri game da illolin tu’ammali da miyagun kwayoyi, wanda da ma darasi ne a cikin manhajar daliban ta wannan shekarar.

Bayan koyarwa a makarantar, Gbajabiamila zai kuma ziyarci wasu ‘yan gudun hijira a sansanin su da ke jihar Katsina, sannan   zai gana da gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari da wasu shugabannin jama’a da kungiyoyin matasa daba-daban.