Home Labaru Kiwon Lafiya Wuraren Kiwo: Samuel Ortom Yay I Barazanar Maka Shugaba Buhari Kotu

Wuraren Kiwo: Samuel Ortom Yay I Barazanar Maka Shugaba Buhari Kotu

42
0
Buhari & Otom

Gwamnan jihar Benue Samuel Ortom, ya ce zai iya gurfana gaban kuliya da shugaba Muhammadu Buhari, matukar ya hakikance a kan dawo da wuraren kiwon dabbobi a Nijeriya.

Samuel Ortom dai ya soki matakin da gwamnatin tarayya ta dauka na farfado da Burtalolin kiwo, ya na mai cewa hakan ya saba wa kundin tsarin mulkin Nijeriya.

Gwamna Ortom, ya ce jihar sa ba za ta amince da wannan shirin ba, ya na mai baraanar maka gwamnatin tarayya kotu matukar ta dage a kan kudirin ta na samar da wuraren kiwon.

A cewar Ortom, filin da ake da shi a Nijeriya ya yi wa jama’a kadan, don haka babu dalilin samar da hanyoyi na musamman da dabbobi za su rika yin kiwo.