Home Labaru Tsaro Takaddama: Hukumar Leken Asiri Ta Tura Sako Ga Lauyan Zakzaky Kan Hana...

Takaddama: Hukumar Leken Asiri Ta Tura Sako Ga Lauyan Zakzaky Kan Hana Shi Fita Waje

63
0
El-Zakzaky

Hukumar Leken Asiri ta Nijeriya NIA, ta shaida wa kungiyar Shi’a ta Nijeriya cewa ba ta karbi fasfo na kasa da kasa mallakin shugaban ta Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da matar sa, Zeenah ba.

Wannan dai ya na zuwa ne, biyo bayan zanga-zangar da kungiyar shi’a da lauya Femi Falana (SAN), su ka yi, a kan kin amincewa da gwamnati ta yi na sakin takardun malamin da iyalin sa.

Ma’auratan dai ba za su samu damar zuwa kasar waje neman magani ba, bayan babbar kotun jihar Kaduna ta sallame su tare da wanke su.

Wata majiya ta ce, Sakataren kungiyar Abdullahi Muhammad, ya tura koke ga manyan kungiyoyin duniya a kan cewa, su sa Gwamnatin Nijeriya ta bi umurnin kotu, sannan ta saki takardun El-Zakzaky da matar sa.