Home Labaru Kisan Jos: Hukuma Ta Sha Alwashin Kama Mazauna Yankunan Da Ake Kashe-Kashe

Kisan Jos: Hukuma Ta Sha Alwashin Kama Mazauna Yankunan Da Ake Kashe-Kashe

51
0
Nigerian Police

Hukumomin karamar hukumar Jos ta Arewa, sun ce za su bibiyi duk mutumin da ya kai hari a kan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba domin fuskantar hukunci.

Sun ce za su kama mazauna unguwa ko yankin da abin ya faru, don tabbatar da abin da ya dace idan wadanda ake zargin su ka tsere.

Wannan dai ya na zuwa ne, bayan harin da aka kai wa matafiya musulmai kusa da hanyar Gada-biyu a karamar hukumar Jos ta Arewa, da kuma tashin hankalin da ya biyo baya a wasu yankuna.

Shugaban Kwamitin Gudanarwa na Karamar Hukumar Jos ta Arewa Shehu Bala Usman ya bayyana haka, bayan bitar dokar hana fita da gwamnatin jihar Filato ta sanya.

Ya ce gwamnatin jihar Filato ta maida hankali wajen samar da zaman lafiya a yankin, ya na mai gargadin cewa gwamnati ba za ta bari wani mutum ko kungiyoyin da ke da niyyar yin zagon kasa ga kokarin ta su cimma burin su ba.