Gwamnan Jihar Zamfara Dauda Lawal ya amince da biyan ma’aikatan Jihar kuɗaɗen su na hutu a matsayin wata garaɓasa ta musamman albarkacin watan Ramadan mai alfarma.
A ranar Laraba ne dai ma’aikatan gwamnatin Jihar da na Ƙananan Hukumomi suka fara karɓar kuɗaɗen hutu.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya fitar a Gusau, ya bayyana cewa kuɗaɗen hutun ma’aikatan shi ne kashi 10 cikin 100 na albashin su na shekara.
A cewar sa, kuɗaɗen hutun da aka biya a matsayin kyautar azumin Ramadan wani shirin jin daɗi ne da aka ba dukkan ma’aikatan gwamnati domin sauƙaƙa wahalhalun tattalin arzikin da ƙasa ke fuskanta.
Sanarwar ta jaddada cewa gwamnatin Gwamna Lawal ta kasance mai son ma’aikata domin kuwa bayan hawan sa mulki, ya biya duk albashin da ma’aikata ke bin gwamnatin da ta shuɗe, ya kuma biya kuɗaɗen garatuti, sannan ya amince da biyan albashin wata 13 ga ma’aikatan jihar.