Home Labarai Tallafin Albashi: Gwamna Bago Ya Amince Da Biyan Karin Naira Dubu 20...

Tallafin Albashi: Gwamna Bago Ya Amince Da Biyan Karin Naira Dubu 20 Ga Ma’Aikata

36
0

Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umar Bago ya amince da biyan tallafin karin albashin na Naira dubu 20  ga dukkan ma’aikatan jihar.

Gwamnan ya aiwatar da shirin ne biyo bayan rokon da shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya yi wa gwamnatocin jihohi su aiwatar da shirin biyan tallafin albashin ma’aikata domin rage musu wahalhalu da tsadar rayuwa da ake fuskanta.

Gwamna Bago ya sanar da fara biyan tallafin albashin ne na Naira dubu 20 a zaman majalisar zartarwar jihar da aka gudanar a gidan gwamnatin da ke birnin Minna.

Gwamna Bago ya bayar da tabbacin cewa, za a gaggauta biyan kudin, inda ake sa ran ma’aikatan za su fara karbar kudaden su tun daga ranar Laraba.

In ba a manta ba, a baya mun bayyana muku cewa a ziyarar da shugaban kasa ya kai jihar Neja, ya roki gwamnonin jihohi su fara biyan tallafin albashin ma’aikata har zuwa lokacin da za a fitar da mafi karancin albashi.

Leave a Reply