Home Labarai Gudumawa: Gwamnatin Tarayya Ta Ba Kano Motocin Kashe Gobara Na Zamani Guda...

Gudumawa: Gwamnatin Tarayya Ta Ba Kano Motocin Kashe Gobara Na Zamani Guda Biyu

127
0

Gwamnatin jihar Kano ta samu gudunmawar motocin kashe gobara na zamani guda biyu daga gwamnatin tarayya domin taimakawa wajen magance bala’o’i na gobara a jihar.

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, a lokacin kaddamar da motocin da hukumar kashe gobara ta tarayya ta ware wa jihar, ya nuna jin dadin sa ga gwamnatin tarayya kan mikawa jihar sa wadannan motoci.

Gwamnan ya kuma bayar da tabbacin cewa, za a yi amfani da su ta hanyar da ta dace, inda ya kara jaddada gagarumin muhimmanci da alfanun da motocin ke da shi ga al’ummar jihar Kano wajen inganta tsaron dukiyoyin al’ummar jihar.

Mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Dawakin Tofa, a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a ranar Alhamis, ya bayyana cewa, gwamnan ya karbi tallafin ne daga hannun Kwanturola na hukumar kashe gobara ta jihar Kano.

Daga nan, Dawakin Tofa ya mika godiyar Gwamnan bisa wannan karamcin, sannan ya kara da cewa, gwamnan ya yi alkawarin samar da kayayyakin da suka dace domin tallafawa Hukumar wajen gudanar da ayyukan ta yadda ya kamata.

Leave a Reply