Home Labaru Kuma Dai: ‘Yan Bindiga Sun Sace Daliban Islamiyya 9 A Jihar Katsina

Kuma Dai: ‘Yan Bindiga Sun Sace Daliban Islamiyya 9 A Jihar Katsina

282
0
Yan Bindida

Rahotanni na cewa, ‘yan bindiga sun sace daliban makarantar Islamiyya 9 a wani kauye da ke jihar Katsina.

Ganau sun tabbatar da yadda ‘yan bindigar su ka shiga kauyen Sakki a kan Babura, inda su ka yi awon gaba da dalibai 8 da malami daya yayin da su ke kokarin komawa gida bayan sun tashi makarantar.

Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar Katsina Gambo Isah ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce  yanzu haka jami’an su na aiki tukuru domin ganin sun kubutar da daliban.

Wani mazaunin garin Muntari Nasiru ya shaida wa manema labarai cewa, ‘yan bindigar sun shiga garin Sakki tare da shan gaban daliban da malamin su yayin da su ke kokarin komawa

 bayan tashi daga Islamiyya.

Ya ce ‘yan bindigar sun yi wa yaran da malamin su guda barazana tare da tilasta masu hawa kan baburan, sannan su ka arce da su cikin daji.

Leave a Reply