Shugaban dakarun Sojin Nijeriya Janar Tukur Buratai, ya ce wasu tsirarun ‘yan siyasar da suka fadi zabe ke da hannu wajen ruruta wutar rashin tsaro a wasu yankunan Nijeriya.
Buratai ya bayyana haka ne a birnin Maiduguri na jihar Borno, yayin da ya karbi bakuncin Kwamitin sojoji na Majalisar Tarayya a Cibiyar Tsare-tsaren Farmaki da ke Maiduguri.
Janar Buratai, ya ce kalubalen tsaron da ake fuskanta a yankunan Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya da ma wasu sassan Nijeriya,ya yi amanna da cewa su na faruwa ne sakamakon yadda zaben shekara ta 2019 bai yi wa wasu dadi ba.
Ya ce wadanda zabe bai yi musu dadi ba, su na kokarin daukar fansa ko huce haushi ta hanyar daukar nauyin masu tayar da fitintinu.A karshe ya bukaci ‘yan Majalisar Tarayyasu ja hankalin irin wadannan ‘yan siyasa su sa kaunar kasar su kafin muradun su na siyasa.