Home Labaru Ta’addanci: ‘Yan Bindiga Sun Hallaka Mutane 20 A Karamar Hukumar Kankara

Ta’addanci: ‘Yan Bindiga Sun Hallaka Mutane 20 A Karamar Hukumar Kankara

506
0

Rahotanni na cewa, wasu ‘yan bindiga sun kai farmaki kan wasu kauyukan karamar hukumar Kankara ta jihar Katsina, suka hallaka akalla mutane 20.

Farmakin da ‘yan bindigar suka kai dai ya shafi kauyukan da suka hada da Karya, da Dan Sabau da kuma Dan Marke.

A lokacin da yake tabbatar faruwar lamarin, shugaban riko na karamar hukumar ta Kankara Anas Isa, ya ce ‘yan bindigar da suka kai harin da adadi mai yawa, sun bude wa jama’a wuta nan take, inda suka yi awon gaba da dabbobi da dama.Anas Isa ya kara da cewa, yanayin yawaitar duwatsun da ke yankin da rashin kyawun hanya, ya sa jami’an tsaro gaza cimma maharan har zuwa lokacin da suka tsere.

Leave a Reply