Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar, ya bayyana zarge-zargen da gwamnatin tarayya ta yi masa ta bakin Ministan Yada Labarai cewa karairayi ne kawai na borin-kunya.
Atiku Abubakar daiya yi raddin ne a kan zargin da Lai Mohammed ya yi cewa, jam’iyyar PDP da Atiku Abubakar su na kokarin kitsa wa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buharizagon-kasa ga
A cikin zargin, Lai Mohammed ya ce,tun da ake siyasa a Nijeriya, ba a taba samun lokacin da jam’iyyar Adawa da dan takarar shugabancin kasa suka rika yi wa gwamnati zagon-kasa kamar yanzu da PDP da Atiku suka fadi zaben shekara ta 2019 ba.
Ya ce jam’iyyar DP da Atiku Abubakar, su na kokarin yi wa Gwamnatin Buhari zagon-kasa ta hanyar ruruta wutar siyasa a tun bayan faduwar su zaben shekara ta 2019.Atiku Abubakar, ya ceborin-kunya ne kawai ‘yan kanzagin gwamnatin Buharike yi, saboda sun ga cewa PDP ta dauko hanyar tona asirin magudin zaben da suka tafka a zaben shekara ta 2019.