Home Labaru Wata Sabuwa: ‘Yan Sanda Sun Kama Masu Gidan Saida Jarirai A Jihar...

Wata Sabuwa: ‘Yan Sanda Sun Kama Masu Gidan Saida Jarirai A Jihar Ogun

90
0

Jami’an ‘Yan sanda sun kama mutane biyu a wani gidan saida
jarirai da wata mata ke gudanarwa bayan kotu ta bada belin ta a
Jihar Ogun.

Kakakin ‘yan sanda na jihar Abimbola Oyeyemi, ya ce wata
yarinya ce da aka yaudara zuwa gidan ta gudu sannan ta kai
masu rahoto.

Dakarun rundunar ‘yan sandan dai sun kai samame tare da ceto
yara mata 10, kuma uku daga cikin su na dauke da juna biyu.

Ɗaya daga cikin waɗanda aka kama har da ‘yar shugabar wurin,
wadda ita ma kotu ta bada belin ta bayan zargin ta da laifin
safarar mutane.

Ɗaya mutumin mai na kasa ne kuma ‘yan sanda na zargin shi ke
yi wa ‘yan matan ciki.