Home Labaru Ta’addanci: ‘Yan Daba Sun Kashe Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda A Jihar Cross...

Ta’addanci: ‘Yan Daba Sun Kashe Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda A Jihar Cross River

86
0

Wasu da ake zargin ‘yan daba ne, sun kashe Mataimakin
Kwamishinan ‘Yan Sanda ACP Egbe Eko Edum a birnin
Calabar na Jihar Cross River.

Rundunar ‘yan sanda ta jihar ta tabbatar da mutuwar ACP
Edum, wanda shi ne kwamandan runduna ta 73 PMF Squadron
da ke Magumeri a Jihar Borno.

Kakakin ‘yan sanda na jihar Cross River Irene Ugbo ta shaida
wa manema labarai cewa, lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe
1:00 na daren Talatar da ta gabata a kan Titin Murtala
Mohammed.

Ta ce Mataimakin kwamishinan ya je Calabar ne domin ziyartar
dangin sa a lokacin da abin hawan sa ya lalace a kan titin.

Marigayin dai ya kira matar sa domin ta je ta ɗauke shi, amma
kafin ta ƙara sa wajen ‘yan daba su ka kai ma shi hari su ka
kashe shi.