Home Labaru Kuma Dai: Tsohon Mataimakin Gwamnan Zamfara Ya Sauya Sheka Daga APC Zuwa...

Kuma Dai: Tsohon Mataimakin Gwamnan Zamfara Ya Sauya Sheka Daga APC Zuwa PDP

257
0

Tsohon mataimakin gwamnan jihar Zamfara Ibrahim Wakkala,
ya sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar PDP.

Wakkala ya bayyana sauya shekar ne yayin wata hira da yay i da
manema labarai a Gusau.

Idan dai ba a manta ba, Ibrahim Wakkala ya kasance
mataimakin gwamnan jihar Zamfara a lokacin mulkin
AbdulAziz Yari.

Yayin da ya bayyana dalilin sa na sauya sheka, Wakkala ya ce
tun lokacin da APC ta rasa mulki a shekara ta 2019, an daina
tuntubar sa a kan abubuwan da ke gudana a jam’iyyar.

Ya ce tun lokacin da gwamna Bello Matawalle ya hau mulki, ya
kasance mai ba shi shawara, musamman wajen magance
matsalolin tsaro.

Wakkala ya kara da cewa, ya rubuta wasikar musamman ga
tsohon maigidan sa AbdulAziz Yari game da shawarar da ya
yanke ta fita daga jam’iyyar APC.

Leave a Reply