Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da tsohon shugaban Karamar Hukumar Olamaboro ta Jihar Kogi Isaac Emmanuel Ekpa.
Makusantantan sa sun bayyana cewa an dauke shi ne ranar Juma’a a Ochadamu ta Karamar Hukumar Ofu a lokacin da yake komawa gida.
Rahotanni sun ruwaito cewa Ekpa na shirin birne mahaifin sa ne bayan ya rasu a lokacin da lamarin ya faru.
Kafafen yada labarai a Najeriya sun ruwaito kakakin rundunar ‘yan sandan Kogi, Williams Ayah, na cewa wasu ‘yan sandan sintiri ne suka tsinci mota babu kowa cikin ta a kan titin Ochadamu.
Bayan sun bincika motar ne kuma suka tsinci katin shaida mai dauke da sunan Emmanuel Isaac Ekpa, a cewar sa.
Rahotanni na cewa masu garkuwar sun nemi a biya su kudin fansa naira miliyan 25, inda aka ce wani dan uwan sa na tattaunawa da su domin neman ragi kan abin da suka nema.