Home Labaru Ta’addanci:’Yan Bindiga Sun Sace Hakimi Bayan Kashe ‘Yan Banga A Neja

Ta’addanci:’Yan Bindiga Sun Sace Hakimi Bayan Kashe ‘Yan Banga A Neja

178
0

‘Yan bindiga sun kashe wasu ‘yan banga 3,wadanda ke kokarin hana su sace wani hakimi a karamar hukumar Rafida ke jihar Neja.

Mazauna garin sun ce ‘yan bindiga a bisa babura sun isa gundumar Madaka da misalin karfe 12 na rana, inda suka yi awon gaba da hakimin Gundumar Zakari Ya’u-Idris, yayin da suka kashe 3 daga cikin ‘yan bangan da suka yi yunkurin taka musu birki.

Rahotnni sun ce hakimin, shine wanda aka taba sacewa a watan Disambar shekarar 2019, har sai da aka fanshe shi da kudi naira miliyan 4.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa ‘yan bindigar sun yi wuf da hakimin ne a yayin da ya je duba iyalai da ‘yan uwan sa bayan da ya samu labarin sabbin maharan.