Shugaban majalisar dattawa Sanata Ahmed Lawan, ya yi bayani a game da abin da ya sa Sanatocin Nijeriya su ke aiki da juna duk da bambancin jam’iyyun siyasar su.
Ahmed Lawan ya yi jawabin ne a wajen wata liyafa da jami’ar tarayya ta Maiduguri ta shirya a karshen makon da ya gabata.
Sanatan ya cigaba da cewa, majalisar da ya ke jagoranta a yau ta na da bambanci da duk sauran majalisun da aka yi a baya, domin ba a la’akari da sabanin siyasa a wajen aiki.
Ya ce jama’a da dama ba su fahimci aikin majalisa ba, saboda ita ce ‘yar autar bangarorin gwamnati, ya na mai cewa burin su kawai shi ne a samar da tsaro da inganta tattalin arziki.
Sanatan ya kara da cewa, aikin su ne yin abin da ya kamata ba tare da nuna bambancin siyasa ba.
You must log in to post a comment.