Home Labaru Wata Sabuwa: Yakubu Dogara Ya Koma Jam’iyyar APC

Wata Sabuwa: Yakubu Dogara Ya Koma Jam’iyyar APC

345
0

Jam’iyyar  APC  jihar  Bauchi ta ce  ta yi babban kamu bayan tsohon shugaban majalisar wakilai Yakubu Dogara ya koma APC.

Shugaban jam’iyar na jihar Bauchi Uba Nana, ya bayyana haka a lokacin da yake magana da manema labarai  a Bauchi, ya ce zuwa yanzun tsaffin shugabanin PDP da dama sun koma APC jihar  Bauchi.

Uba Nana, ya tabbatar da yanzun haka Yakubu Dogara ya zama Dan jam’iyar APC a jihar, saboda haka dukkanin ‘ya’yan jam’iyar sun karbe shi hannun bibbiyu kuma sun san cewar  dawowarsa jam’iyar zai karawa mata gwarin guiwa.

Ya tabbatar da cewar tun fil’azal Yakubu Dogara dan jam’iyar APC ne, amma daga bisani ya kuma PDP , sai dai zuwa yanzun ya koma APC jam’iyar alummar Najeriya.

Uba Nana,  ya kara da cewar da ma babu wata jam’iyar data dace da shi sai APC, kuma ba shi kadai  bane daga jam’iyar PDP suka koma APC, akwai shugabanin PDP da dama wadanda suka koma APC da tawagar su. Shekara ta 2018 ne Yakubu Dogara,  tare da wasu ‘yan majalisa suka sauya sheƙa daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar PDP.