Home Labaru Taron Sulhu: Shugaba Buhari Ya Dawo Nijeriya Daga Kasar Mali

Taron Sulhu: Shugaba Buhari Ya Dawo Nijeriya Daga Kasar Mali

327
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo Nijeriya daga kasar Mali, bayan sa’o’in da su ka kwashe su na taron sirri domin sasanta rikicin siyasa da ya barke a kasar.

Taron ya samu halartar mai masaukin baki Boubacar Keita, da shugaba Machy Sall na kasar Senegal, da Nana Akufo-Addo na kasar Ghana da kuma Alassane Ouattara na kasar Cote d’Ivoire. 

Wata kungiyar tawaye mai suna M5 na jaddada cewa, sai an watsa kundin tsarin mulkin kasar, sannan shugaban kasar ya yi murabus kafin dawowar zaman lafiya a kasar.

Rikicin ya barke ne bayan kotu ta soke sakamakon zaben kujerun ‘yan majalisa 31 da aka yi kwanan nan, inda ta mika nasara ga wasu daban, wanda kungiyar adawar ta yi zargin cewa mutanen shugaba Keita ne.

A cikin wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara ta fuskar yada labarai Femi Adesina ya fitar, ya ce shugabannin ECOWAS sun saurari bayanai daga bakin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan da kuma shugaban kungiyar adawar Imam Mahmoud Dicko.