Home Labaru Dokar Korona: Gwamnatin Kaduna Ta Garkame Manyan Kantina Da Gidajen Cin Abinci

Dokar Korona: Gwamnatin Kaduna Ta Garkame Manyan Kantina Da Gidajen Cin Abinci

276
0

Sakamakon karya dokar Korona, gwamnatin jihar Kaduna ta rufe wasu manyan Kantuna da Otal-Otal da gidajen cin abinci a karkashin jagorancin Kwamishinan kasuwanci na jihar Idris Nyam.

An dai rufe gidan cin abinci na Shagalinku da ke kan Titin Ali Akilu, da Cake House da ke Sabon Tasha, da babban shagon saida abinci da buredi na Big Treat, da 7 Stars Restaurant, da fitaccen gidan saida abinci na Baraka, da Naji Nice duk a hanyar Isa Kaita.

Sauran sun hada da Otel din Top Galaxy, da ke Sabon Tasha, da kuma Epitome Hotel da ke Barnawa

Gwamnatin jihar Kaduna, ta gargadi masu wuraren kasuwanci su tabbatar sun bi dokokin da gwamnati ta shimfida domin dakile yaduwar Korona.