Home Labaru Kalubale: Nijeriya Ta Na Cikin Matsanancin Hali – OPC

Kalubale: Nijeriya Ta Na Cikin Matsanancin Hali – OPC

300
0

Jagoran kungiyar yarbawa ta OPC Oba Gani Adams, ya yi kira ga shugaba Muhammadu Buhari ya yi kokarin ceto ‘yan Nijeriya daga halin da su ke ciki na kuncin rayuwa.

Da ya ke jawabi a wajen wani taron kara wa juna sani a Ikeja da Legas, Gani Adams ya ce yawancin ‘yan Nijeriya su na ruyawa ne cikin kunci da kuma debe tsanmani.

Jagoran kungiyar ta OPC, ya ce akwai bukatar a ce gwamnati ta fitar da sabbin tsare-tsare da kowa zai amfana a Nijeriya.

Ya ce hakika gwamnati ta yi matukar kokari akan tattalin arziki kamar yanda Femi Adesina ya bayyana, sai dai akwai bukatar sake bunkasa tsarin tattalin arzikin Nijeriya.