Home Labaru Wata Sabuwa: Lauya Falana Ya Nemi Gwamnatin Buhari Ta Saki Su El-Zakzaky

Wata Sabuwa: Lauya Falana Ya Nemi Gwamnatin Buhari Ta Saki Su El-Zakzaky

534
0
Ibraheem El-Zakzaky, Shugaban Kungiyar Shi’a Ta Nijeriya
Ibraheem El-Zakzaky, Shugaban Kungiyar Shi’a Ta Nijeriya

Babban Lauya kuma fitaccen mai rajin kare hakkin dan Adam Femi Falana, ya ce tun da gwamnatin shugaba Buhari ta fara bin doka yanzu, Ministan shari’a Abubakar Malami ya yi kokarin ganin an bi dukkan umarnin da kotuna su ka bada a baya.

Lauyan, ya kuma bukaci a saki shugaban kungiyar Shi’a Ibrahim El-Zakzaky da mai dakin sa, wadanda aka kama tun ranar 15 ga Watan Disamba na shekara ta 2015.

Femi Falana, ya kuma bukaci a fito da duk wani da aka garkame ba tare da bin ka’ida ba, ya roki kotu ta haramta wa gwamnati ci-gaba da tsare El-Zakzaky da matar sa.

A karshe Lauyan ya bayyana cewa, gwamnatin ta rusa kujerar da ta hau cewa sha’anin tsaro ya na gaban ‘yancin ‘Dan Adam, wanda da shi ta fake aka tsare wadannan mutanen.