Home Labaru Ciwo Bashi: Victor Attah Ya Nemi‘Yan Majalisa Su Yi Watsi Da Bukatar...

Ciwo Bashi: Victor Attah Ya Nemi‘Yan Majalisa Su Yi Watsi Da Bukatar Shugaba Buhari

538
0
Victor Attah, Tsohon Gwamnan Jihar Akwa Ibom
Victor Attah, Tsohon Gwamnan Jihar Akwa Ibom

Tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom Obong Victor Attah, ya ba ‘yan majalisar tarayya shawara su yi watsi da rokon gwamnatin tarayya na ciwo bashin kudi.

Obong Victor Attah, ya ce idan har da dukiyar man fetur Nijeriya za ta biya bashin nan gaba, to gwamnati ta dana wa kan ta tarko ne.

Tsohon gwamnan, ya kuma ba gwamnati shawarar ta fadada tattalin arzikin kasar nan domin a rage dogaro da man fetur, wanda a cewar sa, shi kadai ba zai iya kawo wa Nijeriya ci-gaban da ake buri ba.

Ya ce idan har jihohi za su rika zuwa ana kasa masu kudin da gwamnatin tarayya ta tara a wata, za su rika ganin tamkar hakkin su ne, amma idan su ka tsaya da kafafun su dole su fadada tattakin arzikin su da kan su.

A karshe ya ba bada shawarar gwamnati ta shiga yarjejeniya da manyan kamfanonin da za su gina hanyoyi a fadin Nijeriya, sannan su maida kudin su daga baya.

Leave a Reply