Home Labaru Ilimi Ilimi: Kungyoyin Daliban BUK Sun Ki Amincewa Da Karin Kudin Makaranta

Ilimi: Kungyoyin Daliban BUK Sun Ki Amincewa Da Karin Kudin Makaranta

501
0

Kungiyar daliban jami’ar Bayero da ke Kano BUK, ta yi watsi da karin kudin makaranta da hukumar jami’ar ta yi, wanda ya hada da kudin dakunan kwanan dalibai da na makaranta.

Hukumar makarantar dai ta sanar da hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Juma’a, 6 ga watan Disamba na shekara ta 2019.

Kungiyar wakilan dalibai da kungiyar dalibai musulmai da sauran kungiyoyin dalibai sun dauki matakin watsida Karin kudin ne a wajen wani taro da su ka gudanar.

Kamar yadda rahotanni su ka bayyana, an samu karin kudin dakunan kwanan dalibai, inda dakin dalibai masu digiri na farko ya tashi daga Naira dubu 12 da 90 zuwa Naira dubu 20 da 90, sai kuma gado babu katifa da ya tashi daga Naira 7 da 90 zuwa Naira 12 da 90.

A cikin wata wasika da shugabannin kungiyoyin su ka sanya wa hannu,  daliban sun yi mamakin yadda aka yi karin ba tare da an tuntube su ba, inda a karshe su ka bukaci hukumar jami’ar su yi bayanin da ya dace a kan lamarin.