Home Labaru Wata Sabuwa: Jam’iyyar PDP Za Ta Rage Yawan Ma’aikatan Ta

Wata Sabuwa: Jam’iyyar PDP Za Ta Rage Yawan Ma’aikatan Ta

247
0
Zaben Kogi: PDP Ta Nada Kwamitin Yakin Neman Zaben Gwamnan Jihar
Zaben Kogi: PDP Ta Nada Kwamitin Yakin Neman Zaben Gwamnan Jihar

Kwamitin amintattu na uwar jam’iyyar PDP, ya sanar da ma’aikatan helkwatar ta da ke Abuja cewa za su rage yawan su, inda tuni ta kafa kwamitin da zai aiwatar da aikin allamar.

Wata majiya ta ce, zancen rage yawan ma’aikatan ne babban dalilin zaman tattaunawa tsakanin ma’aikata da uwar jam’iyyar.

Haka kuma, jam’iyyar ta na shirin biyan wadanda lamari ya sha kudaden sallama kamar yadda dokar jam’iyyar ta tanada.

A cewar takardar yarjejeniya da jami’in kula da jin dadin ma’aikatan jam’iyyar Innocent Nwankwo ya sanya wa hannu, kudin da ake biyan ma’aikatan a kowane wata Naira miliyan 15 ne, kuma yawan ma’aikatan ya kai 96. Nwankwo, ya ce rage yawan ma’aikatan ya zama wajibi, saboda kudin ya yi wa yawa jam’iyyar, ya na mai cewa ba wai talauci ne ya kama su ba, domin su na da gwamnoni 16, da Sanatoci 44, da ‘yan majalisar wakilai 131, da ‘yan majalisun jihohi 390.