Home Labaru Kisan ‘Yan Mata: Kungiyoyin Mata Sun Gudanar Da Tattaki A Birnin Fatakwal

Kisan ‘Yan Mata: Kungiyoyin Mata Sun Gudanar Da Tattaki A Birnin Fatakwal

213
0

Sama da kungiyoyin mata 50 ne su ka gudanar da wani tattaki domin nuna bacin ran su a kan kisan gillar da ake yi wa ‘yan mata a birnin Fatakwal na jihar Rivers.

Gungun matan da su ka shirya zuwa ofishin ‘yan sanda da hukumar tsaro ta farin kaya DSS da kuma fadar gwamnatin jihar da zauren majalisar dokoki ta jihar, su na neman hukumomi su rubanya kokarin su wajen kare rayukan al’ummar jihar Rivers.

Matan, sun kuma bukaci a gaggauta janye tambarin mata masu zaman kan su da aka yi wa ‘yan matan da su ka mutu ta wannan hanya.

Zanga-zangar matan dai ta na zuwa ne, kwana daya bayan ‘yan sanda sun tabbatar da kama wasu mutane uku bisa samun su da hannu a kisan ‘yan matan.