Home Labaru Juyin-Juya-Hali: An Girke Jami’an Tsaro A Ofishin Sahara Reporters Da Ke Lagos

Juyin-Juya-Hali: An Girke Jami’an Tsaro A Ofishin Sahara Reporters Da Ke Lagos

275
0

Jami’an tsaro sun sanya shinge a ofishin jaridar Sahara Reporters da ake wallafawa a shafin yanar gizo a jihar Legas.

Wata majiya ta ce, jami’an tsaro dauke da makamai sun hana mutane shiga ko ficewa daga ginin ofishin jaridar.

Jaridar Sahara Reporters, ta ce matakin ya na da nufin tsoratar da ma’aikatan ta, wadanda ke zanga-zangar a saki mawallafin jaridar kuma shugabana kungiyar gangamin juyin-juya-hali Omoyele Sowore.

A cikin watan Agusta ne, aka tsare Sowore bisa kokarin yin zanga-zangar gama-gari mai lakabin juyin-juya-hali, domin matsin lamba ga gwamnati a kan batutuwan da su ka shafin cin hanci da rashin iya mulki da kuma rashin tsaro.