Home Labaru Fursunoni 240 Sun Tsere Daga Gidan Yarin Kabba A Kogi

Fursunoni 240 Sun Tsere Daga Gidan Yarin Kabba A Kogi

15
0
Jaik Break Kogi

Akalla fursunoni 240 ne su ka tsere daga gidan yarin Kabba da ke jihar kogi, biyo bayan wani hari da wasu ‘yan ta’adda da tsakar dare.

A cikin wata sanarwa da Kakakin hukumar kula da gidajen yari ta Nijeriya Mr Francis Enobore ya fitar, ta ce wani gungun ‘yan bindiga dauke da makamai ne su ka afka wa gidan yarin da tsakar dare.

Shugaban hukumar Halilu Nababa ya bukaci a dauki matakin maida fursunonin da su ka tsere daga gidan yarin, baya ga tsananta bincike domin gano masu hannu a harin cikin gaugawa.

Hukumar, ta kuma bukaci al’ummar jihar da makwafta su bada hadin kai wajen kai bayanan duk wasu da su ke zargi ga mahukunta domin maida fursunonin gidajen yarin.

A shekara ta 2008 ne, Gwamnati ta samar da gidan yarin Kabba da ke daukar mutane 200, yayin da yanzu haka ya ke dauke da mutane 294 ciki har da 224 da ke jiran shari’a, 70 kuma su na matsayin ‘yan gidan yarin na hakika.