Home Labaru ‘Yan Bindiga Sun Kashe Jami’an Tsaron Nijeriya 12 A Zamfara

‘Yan Bindiga Sun Kashe Jami’an Tsaron Nijeriya 12 A Zamfara

23
0
Bandits

Rahotanni na cewa, ‘yan bindiga sun hallaka jami’an tsaro 12 a wani hari da su ka kai a kan sansanin Soji da ke jihar Zamfara.

Wasu majiyoyin tsaro sun tabbatar da cewa, ‘yan bindigar sun kuma kona wasu gine-ginen Sojoji baya ga sace tarin makamai.

Har ya zuwa yanzu dai babu cikakken bayani a kan wadanda su ka kaddamar da harin, wanda bayanai ke cewa ya faru a Mutumji a ranakun karshen mako.

Sojoji dai na ci-gaba da fatattakar maboyar ‘yan bindiga a jihar Zamfara, matakin da ke zuwa bayan katse layukan sadarwa domin magance matsalar da ta addabi jihar da sauran makwaftanta.