Gwamnan jahar Katsina Aminu Bello Masari, ya umarci sakataren gwamnatin jihar Mustapha Inuwa ya shirya zaman tattaunawa tsakanin gwamnati da shugabannin hukumomin tsaro da ‘yan bindiga domin tattauna batun sulhu.
Wata majiya ta ce, gwamnan ya umarci sakataren gwamnatin ya shirya tattaunawar ne a sansanin ‘yan bindigar dake cikin daji, kamar yadda daraktan yada labarai na fadar gwamnatin jihar Abdu Labaran ya tabbatar.
Abdu Labaran, ya cegwamnan ya dauki matakin ne a karshen wani taron masu ruwa da tsaki a kan tsaro daya gudana a ranar Larabar da ta gabata.
Daga cikin mahalarta taron kuwa akwai mataimakin gwamnan jihar Mannir Yakubu, da kaakakin majalisar jihar Tasiu Musa Maigari, da sakataren gwamnatin jihar Mustapha Inuwa, da mai martaba Sarkin Katsina, da shugabannin kananan hukumomi da kuma wakilan Fulani makiyaya.
Masari ya ce a shirye yake ya tattauna da ‘yan bindigar a duk inda suke domin yin sulhu, tare da kawo karshen ayyukan ta’addanci a jihar Katsina.le=L�5Jus