Home Labaru Wata Sabuwa: Dalibai Sun ‘Yan Afrika Ta Kudu Wa’adin Kwana Hudu Su...

Wata Sabuwa: Dalibai Sun ‘Yan Afrika Ta Kudu Wa’adin Kwana Hudu Su Bar Nijeriya

422
0
Kungiyar Dalibai Ta Nijeriya, NANS
Kungiyar Dalibai Ta Nijeriya, NANS

Kungiyar dalibai ta Nijeriya NANS, ta ba ‘yan kasar Afrika ta Kudu mazauna Nijeriya wa’adin daga yau zuwa ranar Litinin 9 ga watan Satumaba su fice daga Nijeriya.

Matakin dai, ya biyo bayan harin da ‘yan kasar Afrika ta Kudu su ka rika kai wa ‘yan Nijeriya da ke zaune a kasar su.

Jami’in hulda da jama’a na kungiyar daliban Azeez Adeyemi, ya ce kunginyar daliban Nijeriya ba za ta jira har sai gwamnati ta dauki mataki a kan lamarin ba.

Ya ce bacin ran ‘yan Nijeriya ya kai makura a kan irin abin da ‘yan kasar Afrika ta Kudu ke yiwa ‘yan Nijeriya da mazauna  can.

Azeez Adeyemi ya cigaba da cewa, a matsayin su na dalibai, sun yi kokarin mantawa da duk abubuwan da su ka faru a baya tsakanin ‘yan Afrika ta Kudu da ‘yan Nijeriya, amma lamarin ya faskara.

Sharuddan da daliban su ka gindaya wa ‘yan Afrika ta Kudu mazauna Nijeriya dai sun hada da cewa, duk wani dan kasuwa da ya ke dan Afrika ta Kudu dole ya daina kasuwanci a cikin sa’o’i 12, sannan duk manyan kamfanonin Afrika ta Kudu da ke Nijeriya dole a rufe su.

Leave a Reply