Home Labaru Kasuwanci Bincike: Najeriya Ta Shiga Wani Mawuyacin Hali – Babban Bankin Duniya

Bincike: Najeriya Ta Shiga Wani Mawuyacin Hali – Babban Bankin Duniya

804
0

Babban bankin duniya ya ce Najeriya na shiga wani mawuyacin hali a hankali sakamakon sakaci da ta yi da harkar noma da kuma dogaro sosai akan danyen mai wanda aka daina damawa da shi a yanzu.

Mataimakin Shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo a lokacin da yake jawabi a wani taro.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya bayar da tabbacin cewa gwamnatin tarayya a karkashin jagorcin shugaban kasa Muhammdu Buhari za ta tabbatar da habbaka tattalin arziki ta hanyar fitar da kayayyaki, na harkar noma da tsaron abinci da samar da ayyuka da kuma rage talauci.

Ya ce har yanzu ma’aikatar noma ce gwamnati tafi ba muhimmanci wanda ya janyo hankulan shirye-shirye da dama a karkashin manufar bunkasa fannin noma.

Babban masanin harkar noma na babban bankin duniya, Dakta Adetunji Oredipe, ya bayyana haka a Abuja, a yayin da yake jawabi a taron noma na Afrika, wanda daya daga cikin bankunan zamani ya dauki nauyi, ya ce ya kamata sarrafa tattalin arziki zuwa fannin noma ya zamo al’ada, ba wai ka’ida ba tunda tattalin arzikin ya zama abin dogaro sosai.

Taron ya samu halartan mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, wanda ya sami wakilcin karamin ministan noma da ci- gaban karkara, Mustapha Shehuri da ministar harkokin mata, Paulen Talen da gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu da Shugaban bankin Sterling Bank Plc, Abubakar Suleiman.

Leave a Reply