Home Labaru Wata Sabuwa: Boko Haram Na Tilasta Aurar Da Mata ‘Yan Shekaru 12...

Wata Sabuwa: Boko Haram Na Tilasta Aurar Da Mata ‘Yan Shekaru 12 A Jihar Neja

6
0
BOKO HARAM

Rahotanni daga jihar Neja na cewa, mayakan kungiyar Boko Haram su na tilasta wa mazauna karamar hukumar Shiroro aurar da ‘ya’yan su mata masu shekaru 12 da haihuwa.

Majiyoyi daga yankunan da lamarin ya shafa sun ce, maharan sun umarce su da kada su yi biyayya ga duk wata hukuma ko gwamnati a jihar Neja.

Wani ganau a yankin da ya bukaci a sakaya sunan sa, ya ce sun samu labari daga ‘yan’uwan su da ke zama a kauyen Kawure, inda tsohon dan majalisar dattawa mai wakiltar mazabar Neja ta gabas David Umaru ya fito.

Ya ce rundunar hadin gwiwa ta sojojji ta yi kokarin tarwatsa mayakan daga kauyen Kawure a baya, amma bayan wani kankanin lokaci su ka sake taruwa a garin, kasancewar sansanin sojojin ba wurin ya ke ba.

Majiyoyi daga yankin sun yi nuni da cewa, a kauyukan Awulo da Kuregbe, mayakan sun tara mazauna yankin da su ka hada da musulmai da kiristoci, sannan su ka ba su umarnin cewa duk yarinyar da ta kai shekaru 12 a yi mata aure.