Home Labaru An Kama Masu Sama Wa ‘Yan Bindiga Hanyoyin Sadarwa A Kaduna

An Kama Masu Sama Wa ‘Yan Bindiga Hanyoyin Sadarwa A Kaduna

6
0
Bandits

Jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, sun kama wani sojan karya mai suna Hayatu Galadima da abokin aikin sa Hamisu Adamu.

Wata majiya ta ce, mutanen biyu su na kokarin shigar da miyagun kwayoyi da alburusai da kayayyakin sadarwa ga ‘yan bindiga lokacin da aka kama su a Kaduna.

A cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafin san a Facebook, Daraktan yada labarai na hukumar Femi Babafemi, ya ce an kama mutanen ne a kan babbar hanyar Gwagwalada zuwa Abuja.

Ya ce an kwato wasu abubuwa daga hannun su, wadanda su ka hada da harsasai 21 da fakiti 16 na sabbin rediyon sadarwa da kuma abin rufe kai mai launin kayan soji guda hudu.

Sanarwar ta ce, yayin da Hayatu Galadima ya yi ikirarin cewa shi jami’in soji ne mai mukamin Lance Kofur kuma ya na aiki a Ibadan, mutanen sun tabbatar da cewa su na safarar haramtattun abubuwa zuwa jihohin Kaduna da Kano.