Home Labaru Biafra: ‘Yan Siyasa Sun Kasa Fita Yakin Neman Zabe Saboda Harin ‘Yan...

Biafra: ‘Yan Siyasa Sun Kasa Fita Yakin Neman Zabe Saboda Harin ‘Yan Ipob A Anambra

6
0
BIAFRA

Hare-haren masu rajin kafa kasar Biafra a kudu maso gabashin Nijeriya, sun sa ‘yan siyasa ɓuya tare da dakatar da harkokin siyasa a jihar Anambra.

Hukumar zaɓe mai zaman kan ta ta kasa dai ta shirya gudanar da zaben gwamnan jihar a ranar 6 ga watan Nuwamba, domin maye gurbin gwamna mai ci Willie Obiano na jam’iyyar APGA.

Tuni dai ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APC Andy Uba da na jam’iyyar PDP Valentine Ozigbo sun dakatar ta yakin neman zaben su zuwa wani lokaci nan gaba.

Bayanai sun nuna cewa, kungiyar ta IPOB ta zafafa hare-haren da har ta kai ga ‘yan siyasa da magoya baya su na ɓoye alamun wata jam’iyya a tare da su.

Wasu rahotannin sun ce, hatta tutar Nijeriya da tambarin kasa ba a bayyana su a jikin wasu gine-ginen don kada a kai hari a wuraren.