Home Labaru Kimiyya Wata Sabuwa: An Sake Bankado Wani Gidan Mari A Jihar Adamawa

Wata Sabuwa: An Sake Bankado Wani Gidan Mari A Jihar Adamawa

1051
0

Jami’an ‘yan sanda sun ceto mutane 15 a wani gidan ladabtar da kangararru da ke Wuri-Hausa a cikin birnin Yola na jihar Adamawa.

Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar DSP Suleiman Yahaya Ngoroje ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce jami’an hukumar sun kai samame gidan ne da yammacin ranar Talatar da ta gabata.

DSP Suleiman Yahaya, ya ce zai bada karin bayani bayan sun gudanar da bincike a kan lamarin.