Home Labaru Hukumar ‘Yan Sandan Nijeriya Ta Yi Wa Manyan Jami’ai 507 Karin Girma

Hukumar ‘Yan Sandan Nijeriya Ta Yi Wa Manyan Jami’ai 507 Karin Girma

270
0

Hukumar kula da harkokin ‘yan sanda ta Nijeriya, ta amince a yi ma wasu manyan ‘yan jami’ai shida Karin girma zuwa mukamin mukaddashin shugaban ‘yan sandan Nijeriya DIG, yayin da biyu daga cikin su ke shirin tafiya hutun ajiye aiki.

A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan Nijeriya Ikechukwu Ani ya fitar a Abuja, jami’an hudu za su maye gurbin hudun da su ka yi murabus daga aiki, kuma za su kasance a cikin tawagar shugaban ‘yan sandan da ta kunshi mataimakan shi bakwai.

Sanarwar, ta ce sabbin mataimakan shugaban ‘yan sandan da suka samu karin girma zuwa matsayin DIG, sun hada da Abdul Dahiru Danwawu, da Lawal Shehu, da Adeyemi Samuel Ogunjemilusi, da Peter Babatunde Ogunyanwo, da Alex Okpara da kuma Celestine Okoye.

Hukumar ta kuma amince da karin girman kwamishinonin ‘yan sanda 14 zuwa matsayin AIG, wadanda su ka hada da Yunana Babas da Dan-Malam Mohammed da Mua’zu Zubairu Halilu da Rabiu Yusuf da Sanusi Nma Lemu da Ahmed Iliyasu da Mohammed Uba Kura, da Zaki M. Ahmed da Gwandu Haliru Abubakar da sauran su.