Home Labaru Adawa: PDP Ta Soki Yunkurin Biyan Gwamnatin Kogi Bashin Naira Biliyan 10

Adawa: PDP Ta Soki Yunkurin Biyan Gwamnatin Kogi Bashin Naira Biliyan 10

332
0
Zaben Kogi: PDP Ta Nada Kwamitin Yakin Neman Zaben Gwamnan Jihar
Zaben Kogi: PDP Ta Nada Kwamitin Yakin Neman Zaben Gwamnan Jihar

Rahotanni na cewa, yanzu haka takaddama ta barke tsakanin jam’iyyun APC da PDP, biyo bayan yunkurin da shugaba Buharai ya na ba gwamnatin jihar makudan kudade da sunan biyan bashi.

Idan dai ba a manta ba, Shugaba Buhari ya nemi biyan jihar Kogi wani tsohon bashi da ta ke bin gwamnatin tarayya da ya kai naira biliyan goma na wasu ayyukan tarayya da gwamnatin jihar ta taiwatar.

Sai dai jam’iyyar PDP ta ce bai kamata a biya kudin a daidai lokacin da ake shirin yin zaben gwamna a jihar ba, ta na mai zargin cewa ana so ne a ba gwamna Yahaya Bello kudin ne domin yin magudin zabe.

Tuni dai gwamnatin tarayya ta mika bukatar biyan kudade gamajalisar dattawa.

 Wani jigo a jam’iyyar PDP Baba Sule ya shaida wa manema labarai cewa, rashin gaskiya ne ya sa tuntuni ba a biya bashin kiudin ba sai yanzu da zabe ya zo.