Home Labaru Wata Sabuwa: An Sace N16m Na Albashi A Ofishin Sakataren Gwamnatin Katsina

Wata Sabuwa: An Sace N16m Na Albashi A Ofishin Sakataren Gwamnatin Katsina

331
0
Gwamnatin Katsina Ba Za Ta Sassautawa Wadanda Suka Kashe Hakimin ‘Yantumaki Ba
Gwamnatin Katsina Ba Za Ta Sassautawa Wadanda Suka Kashe Hakimin ‘Yantumaki Ba

Wasu mutane sun yi awon gaba da makudan kudin albashin ma’aikatan S-Power a ofishin sakataren gwamnatin jihar Katsina Mustapha Inuwa.

Rahotanni sun ce, mutanen sun kutsa cikin ofishin da ke sakatariyar ne a daren Lahadin da ta gabata, yayin da majiyoyi su ka ce yawan kudin da aka sace ya kai naira miliyan goma sha shida.

Wata majiya ta ce an garkame mutane uku da ake zargin su na da hannun a fashin, wadanda su ka hada da ma’aikatan ofishin sakataren guda biyu da kuma mai gadin ofishin.

Lamarin dai ya faru ne, yayin da aka bai ma ofishin sakataren gwamnatin jihar aikin biyan ma’aikatan S-Power da ke koyarwa a makarantun Sakandare da Firamare na jihar Katsina.

Majiyar ta cigaba da cewa, an ajiye makudan kudaden ne a ofishin sakataren gwamnatin domin biyan ma’aikatan hakkokin su, sai dai kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar SP Gambo Isah da mai magana da yawun sakataren ba su maida martani a kan tambayoyin da aka yi masu game da lamarin ba.