Home Labaru Boko Haram: Gwamnan Borno Ya Zargi Sojoji Da Karbar Na Goro

Boko Haram: Gwamnan Borno Ya Zargi Sojoji Da Karbar Na Goro

398
0
Boko Haram: Gwamnan Borno Ya Zargi Sojoji Da Karbar Na Goro
Boko Haram: Gwamnan Borno Ya Zargi Sojoji Da Karbar Na Goro

Tun bayan da gwamna Zulum na jihar Borno ya yi kakkausar suka game da abin da ya kira karbar nagoro da sojoji ke yi a shingayen da su ke kafawa a manyan tituna a fadin jihar jama’a ke ta fadin albarkacin bakin su a kafafen sada zumunta.

Gwamnan dai ya kai wata ziyarar ba-zata ne a wani shingen da sojoji su ka kafa a kan babbar hanya a garin Jimtilo, inda da kan sa ya rika ba motocin da su ka yi cirko-cirko a kan titin hannu.

Sai dai jim kadan bayan kalaman gwamnan, mai magana da yawun rundunar Sojin, Kanar Aminu Ilyasu ya maida martani, inda ya nuna rashin jin dadin sa game da kalaman gwamnan.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, Kanar Aminu ya ce fitowar irin wadannan zarge-zarge daga bakin mutum mai girma kamar gwamna ba komai zai haifar ba illa maida hannun agogo baya.

Duk da cewa rundunar sojin ta ce za ta binciki zarge-zargen karbar hanci, amma Kanar Aminu ya ce sojoji mutane ne masu bin ka’idojin aikin su.

Sanarwar, ta kuma kara da yin kira ga jama’a su kwarmata duk wani abu da su ka ga sojoji na yi wanda bai dace ba.