Home Labaru Ba Dole Ba Ne Buhari Ya Bayyana Kadarorin Sa – Adesina

Ba Dole Ba Ne Buhari Ya Bayyana Kadarorin Sa – Adesina

312
0
Ba Dole Ba Ne Buhari Ya Bayyana Kadarorin Sa - Adesina
Ba Dole Ba Ne Buhari Ya Bayyana Kadarorin Sa - Adesina

Mai magana da yawun shugaba kasa Femi Adeshina, ya ce babu wata doka da ta wajbata wa Shugaba Muhammadu Buhari bayyana wa ‘yan Nijeriya kadarorin sa.

Femi Adesina ya na bayyana haka ne, a cikin wani shirin Turanci mai suna ‘Politics Today’ da gidan talbijin na Channels ke shiryawa.

Adesina, ya maida wa kungiyar SERAP martani ne, wadda ta nemi shugaba shugaba Buhari da mataimakin sa Yemi Osinbajo da gwamnonin jihohi 37 su bayyana wa ‘yan Nijeriya kadarorin su.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, SERAP, ta ce rashin bayyana kadarorin shugaba ya na sanya alamar tambaya dangane da gaskiyar sa da rikon amanar sa. Sai dai mai maganar da yawun shugaban kasa Femi Adesina ya ce ba haka ba ne, ya na mai cewa babu wata doka da ta wajabta wa shugaban kasa ya bayyana kadarorin sa.