Home Labaru Tattaunawar Sulhu: ‘Yan Bindigar Katsina Sun Kara Sakin Mata 10 Da Wani...

Tattaunawar Sulhu: ‘Yan Bindigar Katsina Sun Kara Sakin Mata 10 Da Wani Jinjiri

322
0

A ci-gaba da tattaunawar sulhu da ake yi da ‘yan bindiga a jihar Katsina, yanzu haka ‘yan ta’addan sun kara sakin wasu daga cikin mutanen da su ka yi garkuwa da su, ciki kuwa har da wani jariri.

Rukunin na biyu da ‘yan bindigar su ka sako sun kunshi mata 10 da wani jinjiri, wanda ya bada jimlar mutane 16 idan aka hada da guda biyar da aka sako ranar Lahadin da ta gabata.

Wannan dai, ya biyo bayan rangadin da gwamnan Aminu Bello Masari ya kwashe tsawon mako daya ya na yi, domin tattaunawa da kuma yin sulhu da ‘yan bidigar da ke tada kayar baya a jihar Katsina, wadanda su ma aka saki mutanen su kusan 9 da ake tsare da su.

Ayyukan ‘yan tada kayar baya da su ka hada da kai hare-hare, da kisan jama’a da garkuwa da mutane dai sun ta’azzara a jihar Katsina, jim kadan bayan rahotanni sun nuna cewa an soma samun zaman lafiya a jihar Zamfara, sakamakon fito da tsarin sulhu da ‘yan ta’addan.