Home Labaru Wata Sabuwa: Ambaliya Ta Mamaye Kauyuka 40 A Jihar Adamawa

Wata Sabuwa: Ambaliya Ta Mamaye Kauyuka 40 A Jihar Adamawa

616
0

Rahotanni daga jihar Adamawa na cewa, ambaliyar ruwa ta mamaye akalla kauyuka 40 da ke cikin kananan hukumomi biyar.

Sakataren hukumar bada agajin gaugawa na jihar Adamawa Dakta Muhd Suleiman, ya ce ibtila’in ya biyo bayan saukar ruwan sama mai karfi ne a wasu sassan jihar har na tsawon kwanaki uku, inda mafi akasarin kauyukan da ambaliyar ta shafa su na gabar kogin Benue.

Dakta Suleiman, ya ce kananan hukumomin da ambaliyar ta shafa sun hada da Girei, da Numan, da Fufore, da Yola ta Kudu da kuma Demsa.

Sakataren ya kuma yi gargadin cewa, akwai yiwuwar fuskantar Karin ambaliyar, la’akari da cewa ruwan kogin Benue na ci-gaba da karuwa, lamarin da ya haddasa yankewar hanyoyin kaiwa wasu karin kauyuka na jihar Adamawa.