Wata gobara ta tashi a helkwatar hukumar tattara haraji ta kasa da ke birnin tarayya Abuja, inda ta lakume wani dakin ajiya da ke jikin dakin cin abincin ma’aikatan hukumar.
Mai magana da yawun hukumar Wahab Gbadamosi ya bayyana wa manema labarai cewa, gobarar ta kona dakin ajiyar hukumar da ke kusa da wajen cin abinci.
Wahab
Gbadamosi ya kara da cewa, Jami’an kwana-kwanan da su ka kashe wutar su na
gudanar da bincike akan abin da ya haddasa gobarar.
You must log in to post a comment.