Sojojin Nijeriya sun tabbatar da cewa, Jami’an su sun kai wani hari a wuraren da Miyagun da su ka addabi jama’a ke boye a jihohin Kaduna da Imo.
Wani babban Jami’in yada labarai na rundunar Sojin kasa Kanar Aminu Iliyasu, ya ce Dakarun Runduna ta 342 sun kai samame a inda wasu Miyagu su ke boye.
Aminu Iliyasu, ya ce Dakarun sun afka wa wadanda ake zargin su na garkuwa da mutane ne a Garin Ihie da ke cikin karamar hukumar Ohaji/Egbema a jihar Imo aka kama mutane biyu.
Sojojin dai sun samu mutanen da kananan bindigogin gida da kwamson harsasan da babu komai a ciki.
Haka
kuma, Sojojin sun dira karamar hukumar Jama’a ta jihar kaduna, inda a nan ma
sun kama mutane biyu da ake zargi, wadanda su ma aka same su da kananan
bindigogi da manyan harsasai.
You must log in to post a comment.