Wasu mazauna birnin Tarayya Abuja, sun bukaci wata babbar
kotu ta dakatar da rantsar da zababben shugaban kasa Bola
Ahmed Tinubu.
Mutanen, wadanda su ka samu wakilcin lauyoyin da su ka hada da Anyaegbunam Ubaka Okoye, da David Aondover Adzer, da Jeffrey Oheobeh Ucheh, da Osang Paul da Chibuke Nwachukwu, su na neman kotun ta dakatar da shugaban alkalan Nijeriya ko ma wani daga rantsar da duk wanda ya yi takara a zaben ranar 25 ga watan Fabrairu a matsayin shugaban kasa ko mataimaki.
Sun ce bukatar hakan ta zama wajibi, har sai an warware korafe-korafen zaben da ke gaban kotu, daidai da tanadin sashe na 134 karanmin sashe na 2.
Hukumar zabe mai zaman kan ta ta kasa dai ta ayyana Bola Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar, yayin da Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP da Peter Obi na jam’iyyar Labour su ke kalubalantar sakamakon.














































