Hukumar Alhazai ta Nijeriya, ta amince da ƙarin Dala 250 a
kan kowace kujerar aikin hajjn bana, kamar yadda
kamfanonin jiragen da za su yi jigilar alhazan su ka nema.
Shugaban hukumar Zikrullah Hassan ya tabbatar da haka, yayin wani taron masu ruwa da tsaki na hukumar da ya gudana a Abuja.
Zikrullah Hassan, ya ce bayan tattaunawa da kamfanonin da za su yi jigilar maniyyatan, sun amince da ƙarin Dala 250 a kan kowace kujerar aikin hajji ta wannan shekarar.
Kwamishinan kuɗi da ma’aikata na hukumar Nura Hassan Yakasai, ya ce kamfanonin jigilar alhazan ne su ka buƙaci hakan saboda yaƙin da ake yi a Sudan, lamarin da ya sa dole sai sun zagaya ba za su bi ta sararin samaniyar Sudan ba.
Ya ce kamfanonin jiragen sun ce sai sun yi zagaye na ƙarin sa’o’i biyu, kuma a kowace sa’a jiragen na sha mai na kusan naira miliyan takwas, don haka hukumar da kamfanonin jiragen su ka amince da ƙarin Dala 250 a kan kowace kujera.














































